Wanda ya yi kisan kai da kuskure ne yake biyan diyya – Sheikh Bala Lau
Shugaban ƙungiyar Izala a Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce abin da ya faru ga masu bikin mauludi abin baƙin ciki ne.
A cewarsa, "muna kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya, ɗaukan matakai da ake yi don kawo ƙarshen ta'addanci abu ne mai muhimmanci, amma kare rayuka na da muhimmanci, kar garin neman gyara a fada cikin wata ɓarna."
Shi ma ya nemi a biya diyya saboda "wanda ya yi kisan kai da kuskure ne yake biyan diyya, wanda ya yi kisa da gangan, shi ba maganar diyya - a kan kama shi a yi masa hukunci."
Sai dai ya ce batu ne da ya shafi gwamnati - duk abin da ya faru, bayan binciken ta, ya kamata gwamnati ta biya diyya ga waɗanda aka rasa su," in ji Sheikh Bala Lau.
0 Comments