A biya mutanen da harin ya shafa diyya – Sheikh Ɗahiru Bauchi
A hirarsa da BBC, Sheikh Ɗahiru Uthman Bauchi, wanda shi ne shugaban ɗarikar Tijjaniya a Najeriya, ya ce akwai mamaki a ce an kai irin wannan hari bisa kuskure.
Ya ce akwai buƙatar mahukunta su fito su yi bayani kan yadda lamarin ya faru tare da biyan diyya ga rayukan da aka rasa.
"Muna neman su sanar da mu yadda aka yi aka ƙona mana masu yin mauludi da jiragen sama," in ji Sheikh Ɗahiru Bauchi.
0 Comments