CBN Zai Rufe Opay, Moniepoint, Kuda da Sauran Bankunan 'Online'? Hadimin Tinubu Ya Yi Bayani
Hadimin Shugaba Tinubu ya yi karin haske kan wani rahoto na cewar CBN na shirin rufe Opay, PalmPay, Moniepoint da sauran bankunan 'online
' A cewar Dada Olusegun, rahoton kanzon kurege ne tare da yin kira ga jama'a da su rinka yin bincike kafin yada jita-jita da za ta kashe kasuwa A baya ne CBN ya ba da umurnin rufe duk wani asusun ajiyar kudi da ba a makala masa BVN da NIN ba, lamarin da wasu ke ganin zai shafi bankunan 'online'
makon da ya gabata babban bankin Najeriya ya ba bankunan ajiyar kudi (DMBs) umurnin rufe duk wani asusun ajiyar kudi da ba shi da BVN da NIN daga shekara mai zuwa
Da yawan bankunan 'online' irin su Opay, Palmpay, da Kuda na ba mutane damar bude asusu ta hanyar amfani da lambar waya kawai, ba tare da sanya BVN ko NIN ba. Sabanin bankuna na zahiri da sai kana da BVN da NIN, amma bankunan 'online' sun takaita shiga ko fitar kudi akan naira dubu hamsin a asusu mai matakin tsaro na farko
Dole ne duk masu asusun ajiyar kudi da ke da matakin tsaro na farko ya makala BVN da NIN, kamar yadda yake dole masu mataki na biyu da uku su saka BVN da NIN, gaza hakan zai sa a rufe asusun." Wannan sanarwa ta saka wasu kafofi banda Legit ikirarin cewa babban bankin zai rufe bankunan 'online' saboda masu amfani da su ba sa saka BVN ko NIN a asusun ajiyar su.
wani labarin, hukumar Inshorar masu ajiyar kudi ta Najeriya (NDIC) ta bayyana sunayen wasu bankuna 20 da suka gaza, sannan za ta biya wadanda suka yi ajiyar kudi a bankunan. Hukumar ta bayyana cewa masu ajiya, masu bayar da bashi, da masu hannun jari, za su sami karin naira biliyan 16.16 a kudin da za a biya su,
0 Comments