Kotu ta yanke wa sojoji maza hukunci kan cin zarafin sojoji mata ta hanyar lalata
Wata Kotu a Japan ta samu wasu tsofaffin sojoji uku da laifin cin zarafin abokan aikinsu mata ta hanyar lalata.
Wannan hukunci mai muhimmanci na zuwa ne bayan wata, mai suna Rina Gonoi ta haifar da muhawara tare da janyo hankalin duniya lokacin da ta bayyana labarinta a shafin YouTube a 2022.
Daga nan ne masu gabatar da ƙara a birnin Fukushima suka sake gurfanar da mutanen uku a watan Maris.
Yin magana kan cin zarafi ta hanyar lalata abu ne da mutane ke ƙyama a Japan, kuma ana kallon shi a matsayin abu maras kyawu.
Sau da dama ba a cika jin rahoton irin wannan matsala ba, kuma batun ya janyo hankalin ƙasar ne kawai a shekarun baya-bayan nan, sa'ilin da aka samu rahotannin da suka girgiza al'umma, kamar na Ms Gonoi.
Wannan ne hukunci mafi girma kan cin zarafi ta hanyar lalata da aka zartar a ƙasar, tun bayan da ƙasar ta yi yi gyaran-fuska ga dokokinta kan cin zarafi ta hanyar lalata, wanda ya hada da sake ma'anar abin da ake nufi da fyaɗe da kuma shekarun neman izini.
0 Comments