An Bai Wa Hamata Iska Tsakanin Jami’an DSS da Na NSCDC Kan Dalili 1 Tak, Da Dama Sun Samu Raunuka
An bai wa hamata iska tsakanin jami’an DSS da hukumar NSCDC a jihar Edo yayin da DSS su ka kai jami’insu asibiti Lamarin ya faru ne a yau Litinin 4 ga watan Disamba a cikin asibitin kwararru da ke birnin Benin City a jihar Hargitsin ya jawo raunata mutane da dama ciki har da jami’ar hukumar NSCDC da kuma sauran masu gadin asibitin
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku. Jihar Edo – An samu hargitsi tsakanin jami’an hukumar DSS da kuma jami’an hukumar NSCDC a jihar Edo. Lamarin ya faru ne a yau Litinin 4 ga watan Disamba a cikin asibitin kwararru da ke birnin Benin City a jihar, Legit ta tattaro.
Mutum 2 sun jikkata bayan an kai ruwa rana tsakanin jami'an DSS da na NSCDC. Hoto: DSS/@official_NSCDC. Asali: UGC
Mene dalilin fadan DSS da NSCDC? Hargitsin ya fara ne yayin da jami’an DSS su ka kawo dan uwansu zuwa asibitin bayan ya fadi yayin wani taro wanda ma’akatan asibitin ba su musu tarba mai kyau ba.
The Nation ta tattaro cewa an samu daidaito bayan shiga lamarin da shugaban masu tsaron gidan gwamnati ya yi da kuma hukumar ‘yan sanda. Yayin hargitsin, mutane da dama sun samu raunuka ciki har da masu gadin asibitin yayin da wata jami’ar hukumar NSCDC ita ma ta samu raunuka. Wani daga cikin jami’an DSS ya bayyana yadda abin ya faru inda ya ce ba su samu tarba mai kyau a asibitin ba inda su ke bukatar kulawar gaggawa.
Wane martani asibitin ta yi?
Ya ce: “Mu na cikin wani taro ne yayin da daya daga cikinmu ya fadi, mun dauko shi cikin gaggawa zuwa wannan asibitin amma ba su karbe mu da kyau ba.
0 Comments