An kai mutum 30 da suka ji raunuka asibiti
Shaidan ya kara da cewa sun kai kimanin mutum 30 asibitin garin Buruku.
Ya ce suna Mauludin ne da sunan makarantar Madrasatul Madinatul Ahbab wa Talamiz da ke Ugara.
Ya ce duk shekara sukan yi wannan taron Mauludi, kuma ko a kwanan baya sun yi wani makamancinsa, amma suka sake tsara gudanar da wani a daren Litinin.
A cikin wadanda suka mutu in ji Bello Ugara har da mata da yara "akwai matan aure wanda za ka ga matan ta mutu, jaririnta bai mutu ba. Akwai wanda za ka ga jaririn ya mutu, uwan ba ta mutu ba".
"Akwai kuma yara kanana wadanda sun mutu, akwai matasa su ma sun mutu. Sannan akwai dalibai maza da mata, ba jinsin da bai mutu ba."
Wasu cikin mutanen da suka jikkata a luguden bam din jirgin sojojin Najeriya a Tashar Biri
0 Comments