Ƴan bindiga sun sace mutum sama da 100 a Zamfara

 




Ƴan bindiga sun sace mutum sama da 100 a Zamfara


Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum sama da 100 a wani harin da suka kai a ƙaramar hukumar Maru ranar Juma’a da dare.


Ƴan bindigar sun abka garin Mutunji bayan sallar Isha’i suka kwashi mutanen suka yi daji da su, galibinsu magidanta, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC.


Sun ce wani ɗan bindiga ne da ake kira Damana tare da mutanensa saman babura suka yi wa ƙarin ƙawanya ya tattara mutanen ya shiga daji da su sakamakon gaza biyansa harajin naira miliyan 50 da ya aza masu.


Babu wata sanarwa daga Jami’an tsaro game da harin na ranar Juma’a da dare a garin na Mutunzi.


Amma mazauna yankin da suka tuntuɓi BBC sun ce suna cikin mawuyacin hali.


“Wani babban ɗan bindiga ne da ake kira Damina ya kawo harin bayan sallar Isha’i lokacin da mutane sun taru suna hirar da dare,” a cewar wani mazauni garin da ya ce yana cikin waɗanda aka kama amma ya samu ya tsere hannun yan bindigar .


“Magidanta sun taru a majalisin da suka saba kamar ƴar kasuwar dare, kwatsam zai ga shi ya zo da yaransa suka kewaye mu suka tattara mu suka shiga daji da mu.”


Mazauna yankin sun ce an daɗe ɗan bindigar na addabar yankin yana aza masu haraji kuma ya kawo harin ranar Juma’a ne yayin da ake ƙaƙarin tattara masa kuɗi.


“Muna ƙoƙarin hada kuɗin - mai ashirin da hamsin a tattara amm kwatsam sai ga shi yan bindigar sun shigo sun kwashi mutane”


“Ya tafi da mutum sama da ɗari, kuma yawanci magidanta ne da matasa,” in ji shi.


Ya ce Allah ya tsirar da shi ne sakamakon sanin dajin da ya ji.


Ya ƙara da cewa ɗan bindigar ya abka garin ne bayan wa’adin da ya bayar ya cika mako ɗaya a haɗa masa naira miliyan 50.


Kuma baya ga garin Mutunji da ya nemi a haɗa masa miliyan 50 akwai wasu ƙauyuka a makwabta da ya nemi a haɗa masa miliyoyin kuɗi.


“Ya tilasta wa mutanen garin Kwana su haɗa miliyan 30, da kuma Sabon Garin Mahuta su haɗa miliyan 20 da Unguwar Kawo su bayar da miliyan 10. Miliyan 110 Damina ya ce ƙauyukan su haɗa ma shi,” kamar yadda wani mazauni yankin ya shaida wa BBC.


Mazauna yankunan sun ce ɗan bindigar kusan shi ya ke da iko da yankin, kasancewar babu jami’an tsaro, a cewarsu.


“Yan ta’addar su ke rike da yankin - suna tura mu daji mu yi masu aikin gona, idan kuma mun dawo su shigo gari su dinga cin abinci da nama da shayi da kayan kwalba ba su biya,” in ji mazauna yankin.

Post a Comment

0 Comments