Me ya sa shari'ar zaɓen gwamna ta hana 'yan siyasar Kano barci?
Cikin abubuwan da 'yan siyasar Kano ke yi har da yanka dabbobi don neman taimakon Allah a shari'ar gwamnan jihar
Rashin tabbas da kuma fargabar abin da ka iya faruwa da rayuwarsu ba tare da gwamnati ba na ci gaba da hana 'yan siyasar jihar Kano barci.
Wannan ba sabon abu ba ne a kowace siyasa musamman ta jihohi a Najeriya, inda 'yan adawa ke ruguntsimin komawa jam'iyya mai mulki ba tare da wata kunya ba da zarar an kayar da tasu a akwatin zaɓe.
Sai dai abin da ya bambanta ta Kano da sauran shi ne, jam'iyyar NNPP mai mulki da APC mai adawa na cikin fargabar samu ko rasa mulkin yayin da Kotun Ƙolin Najeriya za ta fara zaman sauraron ƙarar da NNPP ɗin ta ɗaukaka.
Bugu da ƙari, APC ta shafe kusan shekara 10 tana mulkin Kano - tun daga lokacin Rabiu Kwankwaso har zuwa shekara takwas na Abdullahi Ganduje - kafin NNPP ta doke ta a 2023. Saboda haka, kowace jam'iyya na ganin kanta a matsayin mai mulki har zuwa ranar da kotu za ta yanke hukunci.
Ɓangarorin biyu za su san makomarsu ne nan gaba a kotun daga-ke-sai-Allah-ya-isa bayan hukuncin kotuna biyu na baya sun soke nasarar NNPP a zaɓen na watan Maris tare da bai wa Nasiru Gawuna nasara a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Kano.
An ga yadda 'yan siyasar suka fara rige-rige wajen gudanar da yanke-yanke da salloli don neman nasara a shari'ar ta kotun ƙoli, wadda ba ta saka ranar yanke hukuncin ba, amma ana sa ran za ta zauna a watan Disamba.
Kazalika, 'yan siysar NNPP da na APC na jefa wa juna zargin bai wa kotuna cin hanci don a murɗa hukuncin ya dace da kowannensu, duk da cewa suna musantawa.
Babu abin da aka fi tattaunawa a kai tsakanin mutane a wuraren zama kamar yanayin siyasar da jiharsu ke ciki, inda wasu ke tausaya wa NNPP wasu kuma ke goyon APC.
0 Comments