Kotu ta ɗaure waɗanda aka kama da ƙoƙon kan mutum a Najeriya

 




Kotu ta ɗaure waɗanda aka kama da ƙoƙon kan mutum a Najeriya


An yanke wa wasu ƴan Najeriya su biyar ɗaurin shekara 12 a gidan yari bayan kama su da laifin tono ƙoƙon kan wani mutum domin yin asirin yin arziƙi.

Mutanen sun tono ƙoƙon kan ne domin kai wa wani boka, wanda ya ce ana buƙata domin yi musu asirin zama masu kuɗi.

Mutanen waɗanda aka kama su da ƙoƙon kan a cikin wani buhu, sun amsa laifinsu a kotu.

Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotu a jihar Neja da ke arewacin Najeriya cewa mutanen sun zaƙulo gawar ce a wata maƙabarta bayan binne ta na tsawon shekara uku.

“Waɗanda ake zargin sun ce bokan ya musu alƙawarin cewa za a raba dukiyar da aka samu daga tsafin atsakaninsu, inda ya buƙace su da su kawo ƙoƙon kan mutum,” in ji Jaridar Daily Punch.


A cikin watan Satumba ne jami’an tsaro suka kama matasan biyu lokacin da suke ƙoƙarin bai wa wani mutum ƙoƙon kan domin isarwa ga boka.

Wata kotu a garin Minna ta jihar Neja ce ta ce ta kama mutanen da laifin haɗa kai wajen aikata laifi, da yin kutse a maƙabarta da kuma mallakar ƙoƙon kan bil’adama ba bisa ƙa’ida ba.

Sai dai ba a samu nasarar kama bokan ba.

Tsafe-tsafe dai wani lamari ne da aka sani sosai a Najeriya, inda hatta wasu mabiya addinan musulunci da kirista sukan yi imani da shi, kamar yadda bincike ya nuna.

Yawancin sun yi imani da cewa yin tsafi da jikin ɗan’adam na kawo kuɗi, lamarin da ke ƙara iza wutar kashe-kashen mutane kamar mata da yara da masu nakasa domin tsafi.

Haka nan akan samu mutanen da ke shiga sana’ar sayar da sassan jikin ɗan’adam domin samun kuɗi.

Ana kuma ganin cewa talauci da kwaɗayin kuɗi na daga cikin abubuwan da ke iza wutar tsafe-tsafen a Najeriya.

Post a Comment

0 Comments