Ana zargin wani mahaifi da yin tsafi da dansa don kudi




Ana zargin wani mahaifi da yin tsafi da dansa don kudi


Yan sandan Najeriya

Rundunar 'yan sanda a jihar Enugu ta ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa mahaifin yaron ya amsa laifin da ake zarginsa, kuma ya jagoranci tawagar 'yan sanda zuwa wani rafi inda suka kama wani mutum wanda bako ne kuma fasto mai shekaru 95.

A wurin da tsohon ya ke ne aka gano gawar yaron a cikin wani kabari.

Rundunar 'yan sanda ta jigar Enugu ta ce a ranar 20 ga watan Oktoba ne suka kashe yaron mai suna Chidi Onyishi

Kwamishinan jihar Enugu Abubukar Lawal ya umarci sashin bincike na CID da ya gudanar da kwakwaran bincike wanda zai kai ga gurfanar da duk wani da aka samu da laifi a cikin lamarin.

Rahotanni sun ce mahaifin yaron shi kansa ya tona asirinsa lokacin da ya ke magana da mutanen da ya sayar wa yaron ta wayar tarho cewa sun cuce shi, ba su bashi kudin kirki daga cinikin da suka yi kan yaron ba.

Al'amarin ya ba mazauna jihar mamaki

Mazauna jihar Enugu sun nuna matukar kaduwa kan al'amarin.

A cewar daya daga cikin makobtan iyayen yaron ''Wannan labari ne mai sosa rai, mai ban tausayi sosai, tun lokacan da abin ya faru, yaran makobtanmu suke kuka tare da addu'ar dawowar yaron, haka suma matan ungwar sun nuna takaici a kan abinda ya faru''.


Mahaifin yaron fasto ne daga wani gari da ke jihae Enugu, kuma kamar yadda mahaifiyar Chidi Onyishi ta bayana ya shaku da mahaifinsa.

Ta ce ba ta san abun duniyar da ya rufe masa ido, da har ya yi tsafi da dan da ya haifa ba.

Matar ta ce ta yi ta kiransa a wayarsa bayan bacewar yaron amma ya ki daukar kiranta.

Daga baya ya sameta inda ya fada mata cewa ya manta wayarsa a cikin kekensa na a dai-daita sahu.

Ta ce tun daga lokacin ne ta fara zarginsa.

''Daga baya mijina ya dawo gida,ya ce man na shiga cikin daki na daina kuka,kuma ya ce wasu daga cikin matan da na ke kuka a gabansu mayu ne, na yi watsi da maganarsa saboda bacin rai, na ci gaba da kuka sosai a wajan dakinmu tare da sauran mata da suke yi man jaje''. In ji ta

Mahaifiyar Chidi ta ce shi ne da na uku a yaransu kuma yayin da su ka ci gaba da yin adu'a da kuma azumi, ta fita daga cikin hayacinta saboda yawan kuka na tsawon kwanaki.

Kafin aka cafke shi, mahaifin yaron ya shigar da kara a gaban caj ofis din 'yan sanda cewa yaronsa ya bata

Post a Comment

0 Comments